Ga hanyoyi 7 da masana kimiyya suka tabbatar da idan aka bisu ana samun ciki da wuri:
Masana sunce Idan ana son samun ciki da wuri to a yi amfani da folic Acid kamin fara jima’i.
Ana samun sunadarin Folic Acid a Ganye irin su latas, da Kwai, wake, Ayaba, Lemu, da gyada. Kuma ana samun maganin Folic Acid wanda za’a iya tambayar likita idan ba’a samu damar cin wadancan abubuwan ba.
Ciki na shiga da wuri idan mace na Ovulatin.
Zaki gane idan kina Ovulation idan kika ga wani farin ruwa kamar na danyen kwai yana fitowa daga gabanki.
Wannan ruwan yana taimakawa maniyyi ya kai ga mahaifa ya zauna a samu ciki. A daidai wannan lokaci idan aka yi jima’i dake akwai kyakkyawan zaton mace zata dauki ciki.
Babu wata kalar kwanciyar da masana suka ce tana saurin sa a dauki ciki.
Ki ci gaba da kwanciya a gado bayan yin jima’i, hakan na taimakawa wajan daukar ciki.
Yawan yin jima’i akai-akai baya taimakawa wajan samun cikin mace.
Mace ta cire damuwa ta rika motsa jiki da cin abinci me gina jiki da samun isashshen bacci.
Wadannan bayanai mun dakko su ne daga majiyoyi masu inganci wanda likitoci sun amince dasu.