
Gwamnatin Tarayya ta hayyana cewa, har yanzu kasar Burkina Faso bata sako sojoji 11 da jirgin samansu da suka kama ba.
Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan a wajan taron Kungiyar ECOWAS.
A baya dai wasu Rahotanni sun ce an sakosu amma kuma yanzu Gwamnati ta musanta wadancan rahotannin.
Tuggar yace suna tattaunawa kan yanda za’a shawo kan lamatin ta hanyar lalama.