Hukumar kula da muhalli ta jihar Legas ta sanat da kama mutane 9 saboda yin kashi a bainar jama’a.
Kwamishinan muhalli na jihar, Tokunbo Wahab ne ya bayyana hakan inda yace sun dukufa dan ganin sun hana fitsari da kashi a bainar jama’a a Legas dan tabbatar da tsaftar garin.
Ya kara da cewa a baya sun kama mutane 17 saboda yin kashi da fitsari a bainar jama’a da kuma kin amfani da gadar sama da aka ware dan mutane.