Dalibai mata da yawa a jami’ar University of Benin suna zargin wannan malamin me suna Anthony Asekhauno ya musu fyade.
Da yawansu sun hau shafukan sada zumunta inda suka rika bayyana yanda lamarin ya faru.
Wasu sun ce ya rika kayar dasu jarabawa da gangan dan ya samu damar yin lalata dasu.
Abin jira a gani shine matakan da hukumomi zasu dauka akanshi.