Shahararren mawakin Najeriya, Davido ya nuna kuri’arsa bayan yayi zabe a kasar Amurka.
Saidai lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Yayin da ‘yan Najeriya ke yaba masa, ‘Yan kasar Africa ta kudu kuwa zolayarsa suke inda wani yace karya yake a bola ya dauki kuri’ar ya dauki hoto da ita kawai dan yayi karya.