Masu garkuwa da mutane sun kashe malami a Makarantar Kaduna Polytechnic, Dr. Levy Makama Pondu bayan da suka yi garkuwa dashi kuma suka karbi kudin fansa har sau biyu.
An yi garkuwa dashine ranar August 16, 2024 a yayin da yake komawa gida daga gonarsa bayan ya je ya biya ma’aikatansa.
‘Yan uwa da abokan arziki da dalibansa sun hau shafukan safa zumunta inda suke ta bayyana alhinin rashinsa.