Wednesday, January 8
Shadow

Hoto:Wata mata ta kkashe mijinta da Tabarya

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Wata matar aure ta kashe mijinta da tabarya a Kauyen Lafiagi dake karamar hukumar Katcha ta jihar Naija.

Matar me suna Fatima Dzuma ana zargin ta kashe mijinta me suna Baba Aliyu ne ta hanyar kwada masa tabaryar.

Rahoton yace Baba Ali ya auri Fatima ne shekaru 3 da suka gabata amma basu taba haihuwa ba. Saidai tana da da mijinta na farko.

Fatima ta amsa laifinta inda tace ta aikata hakanne saboda kiyayyar da takewa mijinta. Fatima ta kara da cewa ta makawa mijin nata tabarya ne yayin da yake bacci.

Bayan kashe mijin nata, Fatima ta ja gawarsa ta kaita daji inda kuma sai daga baya danginsa suka gano inda yake.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Saurayin wannan shahararriyar 'yar Tiktok din ya saki Bidiyon da yayi làlàtà da ita

Bayan ganoshi an shafe kwanaki 3 Fatima tana cewa bata san abinda ya faru ba, sai daga baya ne ta amsa laifinta.

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *