‘Yansanda a babban birnin tarayya, Abuja sun kama wasu mutane 2 da ake zargi da satar mota kirar Toyota Corolla.
Kakakin ‘yansandan na Abuja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da lamarin inda yace an kamasu ne ranar Juma’a.
Yace an kamasu ne a yayin da suke kokarin sayar da Motar a kan Naira Miliyan 6.5 a Minna.
Wadanda aka kama din sune, Gwaza Bulus san kimanin shekaru 41 da kuma Yahya Amodu dan kimanin shekaru 45.
Ana ci gaba da bincike kan lamarin.