An kama wadannan mutanen da zargin yiwa karuwai 3 fashi da makami.
Lamarin ya farune a titin Adeniran Ogunsanya dake Bode Thomas a Surulere ta jihar Legas.
Ranar 23 ga watan Augusta ne dai wanda ake zargin suka dauki karuwan 3 da niyyar zasu je su yi lalata dasu. Ko da suka shiga wani wuri sai suka tsayar da motarsu suka kwace musu wayoyi da kudade.
Karuwan dai sun kai kara wajan ‘Yansanda inda suka ce sun gane fuskokin wanda suka musu satar.
Kuma an kamasu.
Kakakin ‘yansandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarun.