
Wasu mata sun fita yin zanga-zanga dan nuna goyon baya ga Sanata Natasha Akpoti data zargi kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio da neman yin lalata da ita.
Masu zanga-zangar sun je kofar shiga majalisar tarayya ne suna suke yi zanga-zangar acan.
Saidai tuni ‘yansanda suka watsa musu barkonon tsohuwa inda suka watsa su.
Hutudole ya fahimci cewa, masu zanga-zangar sun je kofar majalisar ne da misalin karfe 8 na safiyar yau, Laraba.