Kungiyar ‘yan Kwallon Najeriya ta Super Eagle tana can a filin jirgin kasar Libya a tsare inda aka hanasu zuwa ko ina.
‘Yan kwallon dai sun je kasar ta Libya ne dan buga wasa zagaye na biyu da kungiyar kwallon kafar kasar ta Libya bayan sun yi nasara da sakamakon 1-0 a zagayen farko da aka buga a Najeriya.
Awanni kadan kamin saukar jirgin na ‘yan Super Eagle a Libya sai aka canja masa wajan sauka zuwa wani birni me nisa tsakaninshi da inda za’a buga wasa.
Bayan saukar ‘yan kwallon Najeriyar sai ba’a basu motar da zata kaisu inda zasu buga wasan ba, sannan rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta yi kokarin samarwa da ‘yan wasan Najeriyar motar da zata kaisu filin wasan amma hukumomin kasar ta Libya suka hanasu fita daga filin wasan.
Ana ganin wannan kamar ramuwa kasar ta Libya ke yi akan abinda suka yi zargin an musu a Najeriya yayin da suka zo buga wasa da Super Eagle.
Kasar ta Libya ta yi zargin ba’a mata tarba me kyau a Najeriya ba sannan an wulakantata.
‘Yan wasan na Libya dai sun sauka a birnin Fatakwal na jihar Rivers ne maimakon Birnin Uyo na jihar Akwa-Ibom inda za’a buga wasan.
Saida aka sake daukarsu zuwa Iyon.
Hukumomin kwallon kafa na Najeriya a wancan lokacin sun musanta yiwa ‘yan kwallon kafar na NFF wulakanci.
Idan dai Najeriya ta yi nasara a wasan da zasu buga da libyar zata iya samun tikitin shiga gasar cin kofin na nahiyar Afrika da za’a buga a kasar Morocco.
A yanzu dai Najeriyar itace ta daya a rukunin da maki 7 inda ita kuma Libya take ta karshe da maki 1.