Wednesday, April 29
Shadow

Ji yanda ta kaya tsakanin Tsohon Minista, Sheikh Isa Ali Pantami da wani daya zargeshi da Shyekye Kirista a ATBU

Wani ya zargi Tsohon Minista, Malamin Addinin Islama, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami da sawa a Shyekye wani kirista a jami’ar ATBU.

Saidai malam ya mayar masa da martanin cewa wannan zancen karyane dan bai taba kashewa ba kuma bai taba sawa a kashe wani ba.

Mutumin ya kawo Rahoton jaridar Punchng da hotunan dalibin da ake zargin malam akai.

Saidai malam yace idan mutumin yana jin yana da hujja akan wannan zargi nasa, ya kai kotu ko kuma ya bayar da cikakkun bayanansa dan shi malam ya kaishi kotu a yi shari’a, malam yace kaga a haka ma idan zargin da ake masa da gaskene, shi mutumin ya taimaki iyalan mamacin kenan sai a hukuntashi.

Karanta Wannan  Manufar Amurka akan Najeriya ta fara Fitowa Fili: Dan majalisar Amurka dake gaba wajan Zuga Trump akan Najeriya, Riley Moore yace abinda suke so da Shugaba Tinubu a yanzu shine ya Karfafa Alaka da Amurkar Tunda yace ba gaskiya bane maganar cewa ana Mhuzghunawa Kiristoci

Saidai wasu sun rika baiwa malam Shawarar ya maka jaridar ta Punchng a kotu da wanda ya masa wannan zargi.

Amma wasu sun baiwa malam shawarar cewa, bai kamata ya biyewa irin wadannan mutane ba har su rika musayar kalamai dasu ba.

Malam dai yace ya biye masa ne saboda yana tunanin ko yana da hujja akan zargin da yake masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *