Mahajji Daga Jigawa Ya Maida Makudan Dalolin Kasar Amurka Da Kuma Riyal Na Kasar Saudiyya Da Ya Tsinta A Makka Ga Mai Shi
Yawan kudaden da Alhajin na Jigawa mai suna Alhaji Abba Sa’adu Limawa ya tsinta a masallacin na Harami, sun kai Dala dari takwas da kuma Riyal dari shida da casa’in, sai takardun kudaden kasar Rasha da yawansu ya kai Rouble dubu goma da dari biyar.
Hakan da ya yi matukar saka mahajjata ‘yan Nijeriya alfahri.
Wane fata za ku yi masa?