Kakakin majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya baiwa matashiya me shekaru 16, Ms. Isabel Anani damar zama a kujerarsa ta kakakin majalisa inda ta jagoranci zaman majalisar.
Ya bayyana cewa yayi hakanne dan nuna goyon baya ga ranar ‘ya’ya mata ta Duniya wadda aka ware dan nuna muhimmanci basu damar yin gwagwarmayar rayuwa da cimma burikansu na rayuwa.
Kakakin majalisar ya bayyana cewa, wannan shine karo na farko da hakan ta taba faruwa a tarihin majalisar.
Yace an zabo matashiyarne bayan an yi tantancewa ta musamman tsakanin matasa mata kuma ita ce ta yi zarra saboda nuna hali irin na shugabanci da jagorancin Al’umma.
Kakakin majalisar ya wallafa hotunan Ms. Isabel Anani a shafinsa na sada zumunta inda yace yayi fatan wannan abu da take yi ya karfafawa sauran matsa gwiwa.