Wasu ‘yan mata da suka dauki hankula a kwanannan su biyu kawayen juna sun je wajan wani mutum dan yin lalata.
Saidai tin da suka tafi wajensa ba’a sake ganinsu ba.
Hakan yasa aka yi kiyasin cewa sun bata.
Saidai daga baya an gano mutumin inda aka kamashi.
Amma ana kan hanyar da za’a kaishi ofoshin ‘yansanda, sai ya yi kokarin tserewa wannan yasa ‘yansandan suka kasheshi.
An gano cewa, mutumin yana da alaka da wata kungiyar Asiri.
Wasu karin bayanai da suka bayyana kan lamarin sun nuna cewa, mutumin ya baiwa ‘yan matan Naira Miliyan daya ne dan su je yayi lalata dasu.
Saidai ashe ajali ne yake kiransu.
Labarin wadannan ‘yan mata biyu dai sai ci gaba da kara daukar hankaki yake, domin kuwa zuwa yanzu an gano gawarwakinsu a kusa a gidan mutumin da ya gayyace su gidanshi dan yayi lalata dasu.
An dai gano gawarwakin kamar yanda wata majiya ta nuna babu kafafu a jikinsu.
Saidai ba’a tabbatar ko na wadancan ‘yan matan bane amma dai na ‘yan mata biyu ne saidai sun fara rubewa.
Ana dai kan ci gaba da bincike har yanzu.