Rahotanni daga jihar Sokoto sun ce ‘yan Bindiga sun kashe babban soja me mukamin Captain tare da wasu sojoji 3.
Sojan me suna Ibrahim Yibranii Yohana an kasheshi ne da sauran abokan aikinsa 3 a karamar hukumar Gudu ta jihar Sokoto din.
Maharan sun yiwa sojojin kwantan baunane a kan titin Kukurau-Bangi inda kuma suka jikkata sojoji 2 da kona motoci 2 na sojojin.