Rahotanni daga jihar Imo na cewa wasu da ake kyautata zaton ‘yan IPOB ne sun kashe ‘yansanda 2 da kuma farar hula 1.
Lamarin ya farune ranar Talata a Titin Oweri Ogikwe dake jihar.
Hakanan dayan mutumin an harbeshine a cikin gida.
Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya farune da misalin karfe 6:25 na safe.
Zuwa yanzu dai hukumar ‘yansandan jihar batace uffan ba kan lamarin.