Kungiyar Al Hilal ta lashe kofin King Cup na Saudi Pro League bayan doke Al Nassr da ci 5-4 a bugun daga kai sai me tsaron gida.
Wannan ne kofi na biyu da kungiyar ta lashe a shekaru biyu a jere.
Abin bai yiwa Cristiano Ronaldo dadi ba a wasan da aka buga jiya Juma’a a filin wasa na King Abdallah.
An kammala wasan Cristiano Ronaldo yana kuka inda abokan wasansa suka rika bashi baki.
Da yawa dai sun ce basu taba ganin Ronaldon a cikin irin wannan halin ba.
A yayin da yazo fita daga Filin, magoya bayan Al Hilal sun rika kiran sunan Messi dan su bashi haushi.
A karin farko a tarihinsa, Cristiano Ronaldo ya kai kwanaki 1200 ba tare da lashw kofi ko guda daya ba.
Saidai duk da basu ci wasan ba, Cristiano Ronaldo ya dauki hankula inda yayi kokarin cin irin kwallon da yaci Juventus lokacin yana Real Madrid, saidai a wannan lokacin bata shiga ba:
Hakanan kuma Cristiano Ronaldo ne ya lashe kyautar takalmin zinare a matsayin wanda yafi kowa yawan kwallaye a gasar.