Hukumar Kwastam ta samarwa da gwamnatin tarayya kudin shiga sa suka kai Naira Tiriliyan 6.105 a shekarar 2024.
Shugaban hukumar, Mr Adewale Adeniyi ne ya bayyana haka a yayin da yake gayawa manema labarai yanda hukumar ta gudanar da ayyukanta a shekarar 2024.
Yace kudin shigar da suka samarwa gwamnatin ya zarta kudin da gwamnatin ta bukaci su samar mata na Tiriliyan 5.079