Saturday, December 13
Shadow

Hukumar NCC ta gano mutum 1 me layukan waya dubu dari(100,000) a Najeriya

Hukumar kula da sadarwa,NCC ta bayyana cewa ta gano wani mutum 1 wanda ke da layukan waya dubu dari (100,000) shi kadaai.

Wakilin Hukumar, Reuben Muoka ne ya bayyana hakan inda ya jaddada cewa ranar 14 ga watan Satumba me zuwa ne rana ta karshe ga kowa ya hada layinsa da lambar NIN.

Yace suna aiki ne tare da ofishin Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu dan dakile barazanar tsaro.

Sannan yace suna aiki tukuru dan hana sayar da layukan wayar da aka riga aka musu rijista.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda jami'in tsaron Civil Defence ke tonawa wani na hannun daman Gwamna Asiri cewa shine ke daukar nauyin Tshàgyèràn dake hana mutane zàmàn Lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *