
Hukumar sojojin Najeriya ta yi bayani dalla-dalla abinda zai faru ga duk farar hular da aka kama yana saka kayan sojojin Najeriya.
Shugaban sashen kula da huldar sojojin da farar hula, Maj. Gen. Gold Chibuisi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.
Yace abinda doka ta tanada shine duk wanda aka kama da kayan sojojin alhali ba soja bane shine sojojin su kamashi su kaishi wajan ‘yansanda ba tare da duka ko cin zarafi ba.
Yace duk sojan da aka kama yana cin zarafi ana hukuntashi.
Yace dalilin da yasa ba’a barin wadanda ba sojoji ba su saka kayan sojoji shine mutane ba zasu tantance sojojin Gaskiya ba.
Yace kuma masu aikata miyagun laifuka da dama na amfani da kayan sojojin wajan cutar da jama’a.