Hukumar ‘yansanda ta PSC ta saki bayanan mutane dubu 10 da suka yi nasarar tsallakewa mataki na gaba a neman aikin dansandan.
Mutane 61,092 ne dai aka ajiye gefe wanda basu tsallake ba zuwa wannan matsayi.
Hukumar tace dan tabbatar da an yi adalci wajan fitar da sunayen ta yi aiki tare da majalisar tarayya, da hukumar tabbatar da an yi raba daidai wajan bada aikin gwamnati, da kuma hukumar ‘yansanda.
Tace ta tabbatar an baiwa kowace karamar hukuma a Najeriya cikin 774 da ake dasu damar wakilci a cikin wadanda aka dauka din.
Shugaban hukumar, Ikechukwu Ani ne ya bayyana hakan.