Wednesday, September 30
Shadow

Farashin Naira zai tsaya akan 1,450 akan kowace dala

Wata hukumar dake saka ido akan farashin kudaden Duniya, Fitch Ratings ta yi hasashen cewa, farashin Naira zai kare akan 1,450 ne akan kowace dala har zuwa karshen shekarar 2024.

Daraktan hukumar, Gaimin Nonyane ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi kan Najeriya da kasar Misra/Egypt.

Ya kara da cewa, har yanzu Naira bata daidaita ba akan farashi daya tun bayan da aka cire tallafin dala.

Yace zuwa shekara me zuwa ma Nairar zata ci gaba da faduwa amma ba zasu iya bayyana a farashin da zata tsaya ba.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Majalisar Jihar Kaduna ta bukaci a kama da hukunta tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai saboda zargin lalata kudin jihar har Naira Biliyan 423

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *