Friday, December 26
Shadow

Hukumar ‘Yansandan farin kaya DSS ta kori ma’aikata 115 daga aiki

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta ce ta kori wasu jami’anta 115 daga aiki, saboda abin da ta kira wasu sauye-sauye da hukumar ke yi.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, a ranar Talata, DSS ta shawarci al’umma su kauce wa mu’amala da jami’an a matsayin wakilan hukumar.

Hukumar ta kuma wallafa sunaye da hotonan jami’an 115 da ta ce ta koran a shafinta intanet.

Bayanan mutanen da hukumar ta fitar sun nuna cewa an kori mutanen ne tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025.

Matakin na zuwa ne bayan da a watan Oktoban da ya gabata hukumar ta kama wasu tsoffin jami’anta biyu bisa zargin amfani sa sunan hukumar suna damfarar mutane.

Karanta Wannan  Kalli yanda wannan mutumin yawa kansa dan ya daina shan taba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *