Saturday, March 15
Shadow

Hukumomin sojin Amurka sun sace kudin da aka ware dan ciyar da sojojin kasar Abinci

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa hukumomin sojin kasa na kasar ana zargin sun sace kudin da aka ware dan ciyar da sojojin abinci.

Sojojin dai na kokawa da basu abinci musamman nama wanda bai dahu ba, sannan kuma abincin ana basu shi kamar na gidan yari babu wani dadi da kayan hadin da ya kamata.

Jaridar Foxnews ta kasar ta ruwaito cewa ana zargin manyan sojojin da karkatar da makudan kudaden da aka ware dan ciyar da sojojin zuwa wata hanya ta daban.

Jimullar dana Miliyan $225 ne aka ware dan ciyar da sojojin kasar a barikinsu daban-daban dake fadin kasar saidai bincike ya nuna cewa daga cikin kudin, an sace dala miliyan $151 inda aka karkatar dasu zuwa wasu gurare daban.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu Ya Tallafawa Ma'aikata Da Ɗalibai Da Gudummawar Motocin Sufuri

Rahoton yace a kowane wata ana biyan kowane soja dala $465 wanda kuma ana cire haraji daga cikin kudin.

Rahoton yace in banda barikin sojojin dake Alaska da Texas an gano cewa a duka sauran barikin sojojin an sace rabin kudin da ya kamata a ciyar da sojojin abinci.

Rahoton yace tun a shekarar 2020 ake zargin aikata ba daidai ba da kudaden da aka ware dan ciyar da sojoji abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *