
Sanata Orji Kalu ya baiwa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare shawarar ya gyara alakarsa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar ta Zamfara ya kaddamar da Makarantar Kimiyya da fasaha da kuma sabuwar ma’aikatar mata ta jihar Zamfara da aka gina.
Sanata Kalu yace alaka me kyau da shugaban kasa, zata sa jihar Zamfara ta kara samun ayyukan ci gaba.
Ya bayyana cewa, ba wai sai Gwamna Dare ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC amma alaka me kyau tsakaninsa da shugaban kasa, zata taimaka sosai wajan ci gaban jihar ta Zamfara.