
Shugaban kungiyar Kwadago, NLC, Joe Ajaero ya bayyana cewa, duk wanda yace zai zama m’aikaci na gari ya rika zuwa aiki kullun to ba zai tsira da ko sisi ba a cikin Naira dubu 70 din da ake biya a matsayin mafi karancin Albashi.
Ya bayyana hakane a Abuja wajan wani taro da aka gudanar.
Yace amma duk da Dubu 70 din ma bata isa, a haka wasu jihohin baa biyan dubu 70 din a matsayin mafi karancin Albashi.
Yace ma’aikata da yawa sun samu ragi ne ma daga abinda suke karba kamin karin Albashin inda yace hakan ya farune saboda hauhawar farashin kayan abinci da kuma harajin da ake cirewa.
Ya kara da cewa, wasu jihohin kuma Naira dubu 5 kawai suka karawa ma’aikatan.