Wednesday, January 15
Shadow

Idan ku ka amince a ƙaro mana tankar yaƙi 50 to a wata biyu za mu gama da ƴan ta’adda – Ministan tsaro

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya nemi Majalisar Wakilai ta saka kuɗaɗen karin tamkar yaƙi guda 50 a kasafin kudin 2025 don magance matsalar ƴan ta’adda a kasar.

Badaru Abubakar ya yi wannan roƙon ne a yau Talata yayin zaman kare kasafin kudin 2025 da kwamitin tsaro na majalisar ya shirya a Abuja.

Ya bayyana cewa, tare da wannan kayan aiki, za a kawo karshen matsalar ƴan ta’adda a cikin watanni biyu.

“Ma’aikatar Tsaro na da alhakin samar da wasu kayan aiki a wasu yankuna, amma ba mu da damar yin hakan.

“Daga abin da mu ka samu a 2024, mun iya samar da Motoci Masu Sulke guda 20 kawai, amma me za su iya yi?

Karanta Wannan  Ka dakatar da shirin shigo da kayan abinci daga kasar waje, saboda tabbas farashin kayan abinci zai yi sauki amma mu kuma kasuwancin mu zai lalace>>'Yan kasuwar Najeriya suka roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

“Idan mu ka samu karin motocin guda 50 da za su shiga dazuzzuka don fatattakar ‘yan ta’adda, ina tabbatar muku, cikin wata biyu za mu kawo karshen matsalar ‘yan bindiga, amma babu tanadin hakan a kasafin kudin 2025.

“Ina fatan wannan Majalisa za ta kara wa Ma’aikatar Tsaro kudi, domin mu iya samar da kayan aiki a wuraren da ke bukata,” in ji shi.0

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *