Friday, May 23
Shadow

Idan kuna son kanku da Arziki kada ku baiwa dan Arewa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 idan kuwa kuka yi hakan to mutuwa zaku yi murus>>Wike ya gargadi jam’iyyar PDP

Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya gargadi jam’iyyar PDP da cewa kada su baiwa dan Arewa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Wike yace irin wannan abin kashe jam’iyya yake.

Yace misali yanzu ita APC idan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala wa’adinsa a shekarar 2031, dan Kudu zata baiwa ya tsaya takara, to a wancan lokacin kuma sai PDP tace itama tunda APC ta ba dan kudu bari ta ba dan Arewa?

Ana zargin dai Wike da Atiku yake duk da be kira suna ba.

Karanta Wannan  A yau ne ake sa ran kasar Amurka zata fitar da bayanai na zargin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da safarar miyagun Kwàyòyì, Saidai fadar shugaban kasa da APC sun ce wannan ba wani abu bane, Duk abinda ya faru kamin Tinubu ya zama shugaban kasa ba'a sakashi a lissafi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *