
Kungiyar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta baiwa Gwamnatin tarayya shawarar cewa su kara kaimi wajan karbar haraji.
Wakiliyar kungiyar, Kristalina Georgieva ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a birnin Washington DC.
Ta bayyana cewa, ya kamata gwamnatin ta yi amfani da fasahar zamani wajan karbar harajin.
Ta bayyana cewa, bayar da shawara irin wannan ya zama dole musamman lura da cewa farashin man fetur da Najeriya ta dogara dashi wajan samun kudin shiga ya fadi a kasuwannin Duniya.