Kanfanin Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) ne ke buga kudin Najeriya.
Kuma kamfanin na zaunene a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
A baya dai akan kai Kwangilar buga kudin zuwa kasashen waje amma a zamanin Mulkin Shugaba Buhari, an buga kudin na Naira a Najeriya.
Saidai a duk sanda aka buga sabbin kudi, ‘yan Najeriya kan yaba inda wasu ke kalubalantarsu, musamman ma dai ta bangaren ingancin Kudin.