
Dan tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha me suna Sadiq ya jinjinawa mahaifin nasa inda yace yana alfahari dashi.
ya bayyana hakane a yayin da aka taso da guguwar sukar mahaifin nashi.
Yace yawanci masu sukar mahaifin nashi suna yi ne saboda hassada da kuma wadanda suka ci amanarsa.
Yace amma mahaifinsu shugaba ne na gari kuma yayi abinda ya kamata a kasarnan.
Guguwar Sukar Janar Sani Abacha ta sake tasowane biyo bayan kaddamar da littafin da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi.