Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa,yana baiwa gwamnatin tarayya shawarar cire tallafin man fetur gaba daya.
Dangote ya koka da cewa farashin gas a Najeriya na da sauki matuka wanda na kasar Saudiyya ma yafi na Najeriya tsada.
Yace kasashe ciki hadda saudiyyar duk sun cire tallafin man fetur din amma an bar Najeriya a baya.
Dangote ya bayyana hakane a wata hira da kafar Bloomberg ta wallafa.
Yace kuma cire tallafin man da baiwa matatarsa dama zai sa a san ainahin yawan man fetur din da ‘yan Najeriya ke sha wanda a yanzu ba’a sani ba.