
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya yace zai yi aiki tukuru dan goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce a shekarar 2027.
Gwamnan ya bayyana hakane a yayin kaddamar da wani shirin noma da kiwo a jiharsa.
Gwamnan yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya warew shirin Naira Biliyan 120 dan karfafa kiwo kuma ya amince a bayar da kaso 50 cikin 100 na kudin.
Yace babu shugaban Arewa da aka yi a baya da ya taba warewa bangaren kiwo irin wadannan makuda kudade duk da cewa yankin Arewa an sanshi da kiwo.
Yace bisa haka suna goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce.
Yace zasu goyi bayanshi ido Rufe dan ya sake zama shugaban kasa a 2027.
“I assure the President that for what he has done, is doing, and will do, Gombe people will follow him to the battlefield blindfolded.
“We will work for his success in 2027. By God’s grace, his re-election is assured,” Yahaya said.
“No Northern leader in 47 years of power considered investing ₦120 billion to transform the livestock sector, despite it being a predominantly Northern industry,” he said.