Monday, April 27
Shadow

Shin wai me yasa ‘yan kudu suke ta fitowa suna nuna Tinubu suke son ya zama shugaban kasa a 2027 wasu ma har cewa suke basu son dan Arewa amma babu wani babba a Arewa dake mayar da martani?

A ‘yan Kwanakinnan mutane da yawa daga yankin kudancin Najeriya sai fitowa suke suna nuna goyon bayansu ga shirin zarcewar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027.

Da ga ciki ma wasu na nuna basa son dan Arewa.

Na bayabayannan shine wanda Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP a shekarar 2023, Ifeanyi Okowa ya fada bayan komawarsa APC.

Karara ya fito yace mutanensa dan Arewa ne basa son zaba shiyasa ma bai kawo jiharsa ta Delta ba a wancan karin, yace yana sane ya ki bin abinda mutanensa ke so na ya goyi bayan dan kudu, inda yace a yanzu yayi dana sani.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda daya daga cikin sojojin Najeriya da kasar Burkina Faso ta kama ya tabbatar da cewa jirgin su tangarda ya samu shiyasa suka sauka a kasar

Sai kuma maganar da ake alakantata da Ministan Abuja, Nyesom Wike inda aka ruwaito yace nan da shekarar 2027 yunwar da zata kama ‘yan Arewa da kansu zasu rika rokon a basu dubu 2 su zabi APC.

Duk da dai bai amsa cewa shine ya fadi wannan magana ba kuma bai karyatata ba, hakan idan ya tabbata shima rainine ga Arewa.

Sai kuma maganar da ake alakanta Ayodele Fayose tsohon gwamnan jihar Ekiti inda shi kuma sukar ‘yan Arewa aka ruwaito cewa yayi inda yace mutanen Arewa ne ke jawowa Najeriya talauci saboda yawan haihuwa.

Duk da wadannan maganganu babu wani dan Arewa babba da ya fito ya mayar da martani ko ya kare yankin.

Karanta Wannan  Akwai matsin tattalin arziki a kasarnan dan haka kada ku tsayawa sana'a ko aiki daya, ku raba kafa dan samun saukin rayuwa>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *