Friday, December 5
Shadow

INEC ta saka ranar fara rajistar masu zaɓe a faɗin Najeriya

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan wata za ta fara yin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar gabanin zaɓukan 2027.

Cikin wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, ta ce za ta fara rajistar masu zaɓen ta yanar gizo a ranar 18 gawatn Agustan da muke ciki.

Hukumar zaɓen ta kuma saka ranar Litinin 25 ga watan Agustan a matsayin ranar fara rajistar a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi da sauran wuraren da ta ware don gudanar da aikin.

INEC ta ce za a riƙa gudanar da aikin ne daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Juma’a.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: An zargi Gwamnati da hannu a tashin Gobarar kasuwar Taminus ta garin Jos

Kan hakan ne hukumar ta buƙaci waɗanda ba su da rajistar su yi amfani da damar wajen mallakar rajistar.

Hukumar ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun yin rajistar zaɓe a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *