
Rahotanni daga jihar Kebbi sun bayyana cewa ‘yan tà’àddà sun kaiwa wani shingen jami’an kula da shige da fici na Immigration hari.
Sun bankawa shingen wuta, hadda masallacin dake wajan aun Qonashi.
A cikin Bidiyon an ga gawar daya daga cikin mutanen dake wajan na ci da wuta.
Lamarin ya farune a Bakin Ruwa dake karamar hukumar Bagudu.
Rahotanni sun ce mutane 3 ne suka rasu a harin.