Shugaban Darikar Tijjaniyya Mahi Nyass ya shawarci Lamido Sanusi da ya yi koyi da kakansa ta hanyar kin amincewa da kujerar sarautar Sarkin Kano.
Sarki Sanusi shi ne jagoran kungiyar Tijjaniyya a Najeriya. An mayar da shi a matsayin Sarkin Kano a karshen watan da ya gabata bayan da Gwamnatin Jihar ta yi wa dokar masarautu gyara inda ta rusa masarautu hudu daga cikin biyar da ke Jihar tare da tube Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
Mista Ado Bayero dai yana kalubalantar tsige shi ne a gaban kotu, kuma yanzu haka yana zaune a karamar fadar Sarkin bisa kin amincewa da umarnin Gwamnatin Jihar.
Sai dai kungiyar ta Islama a wata takarda mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Yuni mai dauke da sa hannun babban shugabanta Mista Nyass ta bukaci Sanusi da ya ki amincewa da mayar da shi matsayin Sarki, tare da yin koyi da kakansa Muhammadu Sanusi wanda aka ce ya ki amincewa da tayin maido da shi bakin aiki bayan da irin haka ta faru da shi.
Hedikwatar kungiyar da ke Koalack a ƙasar Senegal ta nada Mista Sanusi a matsayin jagoran kungiyar Tijjaniyya a Najeriya.
Kakan Sanusi wanda kuma shi ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I shi ne shugaban darikar na farko a Najeriya.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa