Friday, December 5
Shadow

Jam’iyyar ADC ta dauki lauyoyi kusan 100 su kareta a kotu

ADC ta hayo lauyoyi 97 su kare ta a gaban kotu a ƙarar da ta ke zargin APC ce ta shigar.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta hayo tawagar lauyoyi 97 domin kalubalantar abin da ta bayyana a matsayin “karar bogi” da ta ke zargin APC ta shigar da shugabancin rikon kwaryar jam’iyyar, wanda ya hada da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da tsohon Minista, Rauf Aregbesola.

Tawagar lauyoyin, karkashin jagorancin Barrista Mohammed Sheriff, ta bayyana hakan a Abuja a jiya Talata, inda ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da shigar da kara ta amfani da sunayen wasu mutane da ba ‘yan jam’iyyar ADC ba.

Karanta Wannan  Motar kaya ta hàlalàkà masu bikin Easter biyar a jihar Gombe

Wannan lamari ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja tsakanin Sanata David Mark, wanda yanzu shine Shugaban Rikon Kwaryar na kasa na ADC, da reshen jam’iyyar na jihar Kogi.

A wajen taron, Mark ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa karkashin jagorancinsa, ADC za ta yi aiki cikin gaskiya da adalci, ba tare da nuna bambanci ko fifiko ga wani dan takarar shugaban kasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *