
Rahotanni daga zaben kananan hukumomin jihar Osun da ya gabata ya nuna cewa, Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben a kafatanin kananan hukumomin jihar.
Kwamishinan zabe na jihar, Hashim Abioye ne ya bayyana hakan bayan kammala zaben inda yace PDP ce ta yi nasara a kananan hukumomi 30 da mazabu 323 dake fadin jihar.
Yace an samu nasarar kammala zaben cikin nasa.
Yace Jam’iyyu 18 ne suka yi takara a zaben kuma PDP ce ta lashe zaben na kananan hukumomi dana kansiloli baki daya.