
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi sabuwar doka data hana hukumar sojoji ta kasar shiga bukukuwan watan ranar ‘yan Luwadi da Madigo da ranar Tunawa da kisan da akawa Yahudawa watau Holocaust.
Sauran bukukuwan da aka dakatar sun hada dana watan tunawa da tarihin Bakaken fata, dana ranar tunawa da kisan Martin Luther king, da watan tarihin mata da sauransu.
Hukumar tsaro ta kasar Pentagon ta bayyana cewa, ta dauki matakan ne dan bin umarnin shugaban kasar na dakatar a tsare-tsaren daidaito na jinsi.