
Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyun Adawa na NNPP da PDP da ADC na tattaunawa dan hadewa waje daya su kayar da shugaba Tinubu zabe a shekarar 2027.
Hakan ya fito ne daga bakin me magana da yawun jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi.
Ya bayyana cewa yanayin mulkin da APC ke yi a Najeriya baya bayar da sakamakon da ake bukata.
Fan hakane ake bukatar hada kai dan kayar da ita mulki a 2027.