
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya taya Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf murnar zagayowar ranar Haihuwarsa.
Ya wallafa sako a shafinsa na X inda yace yana Taya Abba Murnar zagayowar ranar Haihuwarsa.
Kwankwaso yace ya tuna irin yanda suna yi rayuwa tare da Abba inda ya masa mataimaki na musamman a lokacin yana Gwamna a zangon farko, hakanan sanda ya zama Ministan tsaro ya kuma tafi da abba a matsayin mataimaki na musamman.
Kwankwaso yace bayan nan ma kuma daya sake zama Gwamnan Kano, ya sake dauko abba a matsayin kwamishina kamin daga baya ya zama gwamnan Kano.
Kwankwaso yace sun yi aiki tare dan ciyar da jihar Kano gaba.
inda yace yana masa fatan Alheri.