
Rahotanni daga jihar Rivers sun ce bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da Gwamna Simi Fubara da mataimakinsa da Majalisar jihar, Ya baiwa sojoji umarnin kula da jihar.
Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa sojojin sun kai motocinsu da tankokin yaki gidan gwamnatin jihar.
Sojojin kamar yanda rahoton jaridar Peoplesgazette ya nunar sun tsare Gwamna Fubara a gidan gwamnatin jihar ta Rivers shi da iyalinsa inda suka hanasu zuwa ko ina.
Rahoton yace jim kadan bayan da Shugaba Tinubu ya dakatar da gwamna Fubara, sai sojojin suka kulle duka kofofin shiga da fita na gidan gwamnatin jihar.
Rahoton yace Gwamna Fubara da iyalansa sun yi kokarin tattara kayansu dan ficewa daga gidan gwamnatin amma aka hanasu saboda sojojin sun hana shiga da fita daga cikin gidan gwamnatin jihar.
Rahoton dai yace sojojin sun ce ba’a basu umarnin barin wani ya shiga ko ya fita daga gidan gwamnatin jihar ta Rivers ba.