Monday, December 16
Shadow

Ji matakin da Kasar Iran tace zata dauka akan kasar Israela bayan da Israelan ta sake kai harin da ya kashe sojan Iran din

A jiyane dai muka samu rahoton cewa, kasar Israela ta kai wani mummunan hari a garin Aleppo dake kasar Syria wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa ciki hadda me baiwa kasar Iran shawara akan harkar soji.

A martanin kasar Iran kan harin, Kwamandan dakarun IRGC na kasar Salami ya bayyana cewa, Israela ta saurari harin ramuwar gayya.

A baya dai, irin wannan harin ne Israela ta kai kan ginin ofishin jakadancin Iran wanda ya kashe wasu janarorin soja na Iran.

Hakan yayi sanadiyyar harin ramuwar gayya akan Israela da Iran ta yi wanda ya baiwa Duniya mamaki kuma ya tayar da hankalin kasar Israela.

Karanta Wannan  Amurka za ta tallafa don sake gina makarantu da asibitoci a Gaza - Biden

A wannan karin dai ba’a san wane irin harin ramuwar gayyane Iran zata kai akan Israela ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *