A yayin da masu amfani da shafukan sada zumunta suka radawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sunan T-pain.
Sunan dai ya watsu sosai inda har tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shima ya kirashi da sunan.
T-pain dai shahararren mawaki ne a kasar Amurka amma ‘yan Najeriya sun lakabawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shi.
A sakon da ya fitar kan cire tallafin man fetur, Atiku Yace T-pain watau Tinubu be damu da wahalar da ‘yan Najeriya ke ciki ba.