
A yankin Oriendu na jihar Abia, mutane na cikin fargaba da tashin hankali bayan da aka rika tsintar gawarwakin mutane musamman mata wadanda aka cire musu al’aura.
Lamarin ya fara faruwane tun daga shekarar data gabata.
Basaraken yankin, HRH Eze Philip Ajomiwe, ya tabbatarwa da jaridar Leadership hakan.
Yace ‘yan sa kai sun kasa magance matsalar saboda mahara da ame zargin matsafa ne na da muggan makamai.
yace dan haka suna kira da gwamnati data kai musu dauki.