Tuesday, May 13
Shadow

Ji yanda aka kama wasu da suka sàcè yaro me shekaru 6 suka yi gùndùwa-gùndùwa dashi dan yin tsafin samun kudi a jihar Gombe

A jihar gombe, jami’an ‘yanssnda sun kama wasu mutane 8 da ake zargi da hannu a cikin yin garkuwa da kashe wani yaro dan shekaru 6.

Wadanda ake zargin sun sae yaronne me suna Muhammad Ibrahim Bulama daga gidan kakansa.

Sannan suka masa yankan rago suka raba gawarsa gida biyu suka kaiwa wani matsafi da yace zai musu asirin kudi.

Wadanda ake zargin sune Magaji Adamu (Wazam), 45, Babayo Musa, 18 years, Jibrin Muhammad (Alias Ya’Haji), 40, Usman Abubakar Khalla, 37, Sadam Umaru, 28, Idris Dayyabu, 45, Abdulrauf Hussaini, 33,Isiyaku Muhammad, 39.

Dukansu sun amsa zarge-zargen da ake musu.

Kakakim ‘yansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace zasu ci gaba da bincike da tabbatar cewa an yiwa wadannan mutane hukuncin da ya dace dasu.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Matashiya ta hau gini me tsawo ta fado ta mùtù bayan da aka hanata shigar banza a kasar Iràn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *