
Dan gidan Peter Obi, Oseloka Obi yayi martani kan zargin da ake masa cewa shi dan luwadi ne.
Hotuna da yawa sun watsu a kafafen sada zumunta inda ake bayyana cewa, Oseloka Obi dan Luwadi ne.
Saidai a martanin da yayi a kafar sadarwarsa yace shi ba dan Luwadi bane kawai ana masa wannan kazafi ne saboda mahaifinsa dan siyasa ne.
Hotunan Oseloka Obi da wani da ake cewa Na miji ne da ya canja halittarsa zuwa mace sun watsu inda ake zargin suna luwadi ne.
Saidai Oseloka Obi yace duk karyane.