Wani magidanci dan shekaru 32 ya kashe kansa a garin Kemta dake Abeokuta jihar Ogun.
Lamarin ya farune da misalin karfe 10 na daren ranar Laraba kamar yanda kakakin ‘yansandan jihar, Omolola Odutola ya tabbatar.
Matar mamacin ce ta iskeshi a rataye ba rai.
‘Yansanda sun so su yi bincike amma iyalan mamacin suka kwace gawar suka ce zasu binne saidai hukumar ‘yansandan tace tana bibiyar lamarin.